8 Agusta 2023 - 07:31
An Sako Wasu 'Yan Kasar Bahrain Uku Da Suka Halarci Muzaharar Kin Jinin Kona Kur'ani

Hukumomin gwamnatin Al Khalifa sun saki Majid Abdul Muhsen, Munir Mushaimea da Ali Mehna, wadanda aka gayyace su a ranar Juma'a 4 ga watan Agusta, 2023 tare da tsare su na tsawon kwanaki 3 bayan an gabatar da su ga mai gabatar da kara.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, An kama wadannan mutane tare da daure su a gidan yari saboda halartar zanga-zangar la'antar kona kur'ani.

@abna24